Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta
Ahlul-Baiti (A.S) ya jaddada kula da ladubban kafafen yada labarai da gaskiya a
kafafen yada labarai yana mai cewa: A kasashen yammaci ba su yi imani da
wajabcin halayya mai kyau ba a kafafen yada labarai ba. Turawan Yamma suna da
ra'ayin Machiavellian a wannan fanni cewa ya kamata a yi amfani da kowace hanya
don cimma burin. Amma mun yi imanin cewa kyawawan halaye da gaskiya ya kamata
su mamaye ayi anfani da su a ko'ina.
Yayin da yake ishara da ganawar da shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya ce: A yayin ganawar da shugaban kasar ta Venezuela, na shaida masa cewa daya daga cikin abubuwan da suka shafi ilimin Ahlul-Baiti shi ne na hankali. Mu gabatar da addinin hankali ta hanayr anfani da hankalin addini. Wani bangare na tarbiyyar Ahlul Baiti (a.s.) shi ne ruhiyya, ko shakka babu wannan ruhiyya dole ne ta ginu a kan duniyar gaibu ne.
Babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul Baiti (A.S) ya bayyana adalci a matsayin daya daga cikin fitattiyar sifa ta mazhabar Ahlul Baiti (A.S) sannan ya fayyace cewa: Tabbatar da adalci shi ne fata da burin dukkan annabawan Ubangiji kuma wannan ba wai abun da aka tilastawa wani akai ba ne sai dai su kansu al’umma bisa zabin kansu za su tsayu Domin a aiwatar da adalci a cikin al'umma wanda kuma dole ne a sauke nauyin hakan.
Ayatullah Ramazani ya ci gaba da jaddada wajibcin kula da hakkin bil'adama da kin zaluncin da ake yi wa bil'adama yana mai cewa: A yau muna fuskantar bautar zamani, ta yadda za a bautar da kasa cikin sarkakiya. Dole ne mu tsaya tsayin daka kan wadannan barazanar kuma daya daga cikin bangarorin labaranmu dole ne ya kasance yana yaki da bautar zamani ne da wariyar launin fata. Fuskantar sabon mulkin mallaka da kuma kula da adalci ya zama dole ga dukkan bil'adama. Ya kamata mu san adabin duniya da harsunan duniya kuma mu kula da shi. A Jihadin bayyanawa ya kamata a jaddada kiyaye 'yancin kai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin uwar duniyar musulmi.
Babban Sakatren majalisar duniya ta Ahlul-baiti (AS) ya bayyana cewa, bai kamata a mayar da abu mai tsarki ba marar tsarki in ya bayyana cewa: Wannan yana daga cikin abubuwan da ake yi a kasashen yamma. Amma akwai wasu kirista ba sa adawa da cin zarafin Annabi Isa (A.S), amma mu muna adawa da irin wannan cin zarafin. Ya kamata ra'ayinmu ya kasance na kasa da kasa kuma hanyoyin martani da gyara ga al'adun yammacin Turai suna yiwuwa ne ta hanyar fahimta da nazarin wannan al'ada. Idan har za mu iya mayar da adabin Ahlul Baiti zuwa yamma, za mu yi nasara.